AL'ADAN MATA A DUNIYA

10 Aug 2018 - 05:51 0 Komentar


ⓂAL'ADAN MATAN DUNIYA 01

ⓂMata kamar yanda muka sani ne jikin mace yana samun canji lokacin al'ada. Kamar qarin sha'awa, kasala, ciwon gabobi, cikowan qirji, kumburin ciki, atini dss. Wanda wasu suna shan wuyan sa wasu kuma basa sha, wato kowa da nata. Amma wasu suna samun matsala ne saboda rashin kulawa. A matsayin ki na mace ya kamata a ce kin karanci kanki, kuma kin karanci abun da zaki yi wurin sau 480 a rayuwar ki koma fiye. Don haka ki san waďannan:

Ⓜ1. Qarin sha'awa: Idan lokacin al'adar ki ya gabato ko ya zo zaki iya samun qarin sha'awa a jikinki. Wanda wannan ba komai bane, domin hormones progesterone da suke limiting libidon ki sun yi qasa sosai. Sai ya sa ki rinqa yin sha'awa sosai. Sai ki tsare kanki daga maza.

Ⓜ2. Samun cikakken hutu: Hormones suna yin qasa sosai. Wanda su suke kare jikinki daga wasu abubuwa. Sai qarfinki ya ragu, don haka kwanciya da samun hutu zai taimake ki sosai. Domin aiki in yayi yawa zaki iya jin jiri, koma ki yanke jiki ki fadi. Da rage shiga rana ko yawo.

Ⓜ3. Cin abincin da ya kamata: Akwai abincin da zaki ci da zasu rage ciwo, kasala dss. Kamar wake da yake dauke da sinadarin fiber. Wanda yana iya kare ki daga bacin ciki lokacin jinin, ko matsewar bayan gida. Sai legumes da suke dauke da vitamin B mai yawa. Wanda zai rage miki kasala da jin ba dadi.

ⓂKoren kayan lambu wadanda suke ďauke da magnesium, calcium da potassium wanda suke rage, ko hana jin ciwo ko zafi lokacin al'ada. Haka nan akwai masu ďauke da Vitamin K wadanda suke iya hana zuban jini mai yawa ko gudajen jini. Sai abinci masu dauke da Omega-3 fatty acids, wanda in mace na cin su sosai suna hana alamomin zuwan jini na ciwuka baki ďaya. Sai cin dabino da zuma wanda yana rage ciwon ciki dss.

Ⓜ4. Sannan sai shan isashen ruwa, tare da shan ruwan dumi. Da shan abubuwa masu dumi da dumama jiki. Waďanda za su taimaka wurin fitar da jinin da sauki. Kamar herbal tea, ko tea mai citta da kayan qamshi, green tea, black tea dss. Musamman in cikinki na ciwo. Sai dafa hulba a ďan zuba zuma a sha da dumi. Shima yana rage ciwon ciki.

Ⓜ5. Amfani da ruwan dumi duk in za ki yi tsarki: Wanda zai sanya ki jin saukin ciwo ko wani tsunguli. Kuma duk in kin tashi yin tsarkin, ki rinqa wankewa daga gabanki zuwa wurin bayan gida (anus). Wato duka zaki hada ki dauraye. Ki ďan tsane wurin ki mayar da pant. Wannan ruwan dumin zai hana duk wasu kuraje da zaki iya samu a wannan lokacin. Sannan zai kare ki daga cututtuka.

Ⓜ6. Yin wanka a kai a kai: Zai rage miki jin wasu yanayi kamar 'bacin rai da rashin magana. Kuma zai taimaka wurin fitan jinin. Sannan in har kin shiga rana mata a koyi yin wanka. Musamman lokacin al'ada, wasu sai ka ji kamar zaka yi amai saboda abun ya hadu biyu.

Ⓜ7. Canza pad (auduga): Ki tabbata kin za'bi product mai kyau kuma wanda ya dace da irin zuban jininki. Domin in kina zubar da jini da yawa to akwai wadanda ko kin sa ba za su riqe ki ba. Sannan sai canzawa aqallah duk bayan awa hudu zuwa 5. Kuma ko jini ya ta'bi pant ko bai taba ba, in kin tashi canzawa ki haďa da wando baki daya. Saboda guje ma wari da infections.

Ⓜ8. Mentrual Pants: Amfani da su na da amfani. Domin sun yi musu wurin da zai hana pad matseki. In baki da shi ki nemi cotton sakakku wadanda basa matse ki da yawa. Su zaki rinqa amfani da su lokacin al'ada.

Ⓜ9. Motsa jini kadan: In kin huta ki dan motsa jininki.

Eza Controller

 • Sunting
 • Hapus
 • Komentar

  0 Tanggapan dari "AL'ADAN MATA A DUNIYA"

  Komentar baru  Please refresh...

  Smiley
  DRAMA KOREA TERBARU

  aplikasi youtube downloader